Advertisement

Responsive Advertisement

Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen Kwankwaso Ta Karshe Ke Gudana Yau A Kanon Dabo


 Jirgin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP, 

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso Zai Sauka Tasha Yau A jihar Kano. 

Kwankwaso wanda ya mulki Kano har sau biyu zai karkare kamfensa a mahaifarsa. 

Tawagar kamfe ta isa Na'ibawa, Zaria Road 

Tawar kamfen Rabiu Musa Kwankwaso ya isa Na'ibawa, Zaria Road, inda yan daba suka far wa mabiyansa 'dazu da rana. 

Dare yayi yanzu kuma ko fara taro ba'a yi ba. 

Matasa da goraye da takkuba sun na cikin tawagar kamfe 

An hango wasu matasa dauke da goraye da takkuba yayinda Sanata Rabiu Kwankwaso ke cikin karamar hukumar Kura ta jihar. 

Kamfe da wadannan makamai ba sabon abu bane a siyasar jihar Kano. Gabanin haka, wasu yan baranda sun kaiwa wadanda suka je tarban Kwankwaso hari a na'ibawa Zaria road. 

Har yanzu tawagar Kwankwaso na Kura 

Tawagar Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso har yanzu bai isa cikin birnin Kano saboda yawan jama'an da suka tarbesa. 

Kwankwaso ya isa Bebeji tun kafin lokacin Azahar amma har yanzu bai samu shiga birnin Kano ba. Yanzu haka dai tawagar na Kura. 


Na dira Kano lafiya, na ya'da zango garin Kofa 

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa ya dira jihar Kano lafiya kuma ya ya'da zango karamar hukumar 

Bebeji inda ya samu tarbar dinbim mabiya. Kwankwaso ya yi kira da mabiyansa kada su tanka masu tada tarzoma kuma su bi doka da oda. 

A jawabin da ya daura a shafinsa na Tuwita yace: "Mun biya garin Kofa dake karamar hukumar Bebeji yayinda muke hanyarmu ta zuwa Kano. 

"Soyayyar da aka nuna mana gagaruma ce. Ina kira ga mabiya su kasance masu bin doka yayinda za'a cigaba da taro," 

Post a Comment

0 Comments