Advertisement

Responsive Advertisement

Mutane Sun Ci Gaba da Kai Tsohon Naira Bankuna Yayin da CBN Ya Bar Shafi a Bude


Kwastomomin bankuna sun ci gaba da maida kuɗinsu cikin daɗin rai yayin da CBN ya bar shafin maida kuɗin a bude 
Har ranakun karshen makon nan Fotal ɗin CBN na nan a bude kuma mutane sun yaba da yadda bankuna suke sauraronsu 
Sai dai akwai wadanda ke fuskantar matsaloli yayin maida tsoffin kuɗinsu duk da sun bi matakan da aka gindaya 
'Yan Najeriya sun ci gaba da tururuwar zuwa bankunan kasuwanci domin maida tsoffin takardun N500 da N1000 a ranar Litinin 20 ga watan Fabrairu, 2023. 
Leadership tace lamarin ya zo da sauki yayin da babban bankin Najeriya ya bar shafin yanar gizo na cike Fam ɗin maida tsoffin kuɗin a buɗe.
Har zuwa daren ranar Litinin shafin a buɗe yake ga kowane ɗan Najeriya mai niyyar tarkata tsoffin kuɗin da aka haramta ya maida su banki don gudun asara.

Post a Comment

0 Comments