Dan takarar shugabancin Najeriya ƙarkashin jam’iyyar NNPP Injiya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yi mamakin yadda ya ga wasu gwamnonin APC ke zagi ko sukar shugaban ƙasar kan sauyin kuɗi.
A wani sako da ɗan takarar ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce bai taɓa tunanin cewa za a kai matakin da wasu daga cikin gwamnonin za su fito su riƙa zagin shugaba Buhari ba.
‘’Haƙiƙa na yi mamakin yadda waɗannan abubuwa suke faruwa, kuma abin sai ya ba ka mamakin me ke damunsu?’’
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce watakila kuma maganar EFCC - cewa wasu daga cikinsu sun ɓoye biliyoyin kuɗi a gidajensu- haka take.
‘’Dan haka wannan tsari da aka zo da shi, zai mayar da biliyoyin kuɗin da suka sace tamkar yayi ko takardu marasa amfani, ina ga wannan shi ne dalilin da ya sa suka fusata’’, in ji Kwankwaso
Ya ƙara da cewa gwamnonin ba suna yi ne don ƙaunar talakawansu ba, domin kuwa a cewarsa babu wani dalili ko hujjar da suka nuna cewa suna ƙaunar talakawan nasu.
Kwankwaso ya kuma ce jam’iyyarsa za ta taimaka wa gwamnatin tarayya musamman a ranar zaɓe wajen sanya idanu domin taimaka wa EFCC da ‘yan sanda da sauran hukumomi wajen fallasa masu amfani da kuɗi domin sayen ƙuri’a.
0 Comments