Nan gaba kaɗan ne a yau za a mayar da gawar ɗan wasan Ghana Christian Atsu zuwa gida daga Turkiyya inda ya mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta afka wa wani yanki na ƙasar.
A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta fitar ta ce gwamnatin ƙasar na gudanar da shirye-shirye domin tarbar gawar ɗan wasan.
Ana sa ran isar gawar zuwa ƙasar da misalin ƙarfe 7:40 na maraicen ƙasar kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Gawar Atsu za ta isa Ghana ne a jirgin Turkish airlines tare da rakiyar jakadan Ghana a Turkiyya da kuma iyalan ɗan wasan.
Sanarwar ta ce gwamantin ƙasar tare da hukumar wasannin ƙasar ne za su tarbi gawar a filin saukar jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa da ke Kotoka.
Daga ƙarshe sanarwar ta miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan ɗan wasan tare da addu'ar neman gafara a gare shi.
Atsu dai ya rasu ne sakamakon girgizar ƙasar da ta afka wa Turkiyya da Syria kusan makonni biyu da suka gabata.
A ranar Asabar ne wakilin ɗan wasan ya bayyana gano gawarsa a ƙarƙashin ɓaraguzan gidansa kwaniki 13 bayan afkuwar girgizar ƙasar.
Atsu mai shekarar 31 ya yi wasanni a ƙungiyoyin Chelsea da Newcastle.
0 Comments