Allah ya kawo mu.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa'ad Abubakar III (Sultan na Sakkwato) ya fitar da sabuwar sanarwa.
Sultan ya umarci ɗaukacin al'ummar Musulmai a Najeriiya su fara duba jinjirin watan Sha'aban 1444 AH daga ranar Litinin 29 ga watan Rajab, 1444 daidai da 20 ga watan Fabrairu, 2023.
Sarkin Musulmin ya ba da wannan umarni ranar Lahadi a Sakkwato a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin harkokin addini na fadar Sultan Sakkwato.
Bayan haka Sultan ya roki Allah SWT ya shiga lamarin Musulmai ya basu karfin ikon sauke hakkoki da nauyin da addini ya ɗora masu.
Watan Sha'aban shi ne wata na 8 a cikin jerin watannin Kalandar Musulunci kuma shi ne watan da Ramadan ke biye masa.
0 Comments