Advertisement

Responsive Advertisement

Tashin Hankali Yayin da Wata Sabuwar Girgizar Kasa Ta Afkuwa a Kan Iyakar Kasashen Turkiyya da Siriya


 An sake samun wata mummunar girgizar kasa a kasashen Siriya da Turkiyya da yammacin Litinin 20 Faburairu, 2023 

An ruwaito cewa, an samu raunuka masu yawa, kuma girgizar na zuwa ne makwanni biyu bayan faruwar ta farko da ta kashe mutane sama da 40,000

 Ba wannan ne karon farko da aka fara samun girgizar kasa a wasu kasashen waje ba, hakan ya sha faruwa a lokuta daban-daban 

Siriya - An sake samun wata sabuwar girgizar kasa da ta auku a iyakar kasashen Turkiyya da Siriya, kwanaki bayan afkuwar ta faro da mutane sama da 40,000 suka kwanta dama a kasashen biyu.

 A cewar kamfanin dillacin labaran Sriya na SANA, girgizar kasar mai girman 6.4 ta daki yankin Hatau ne na kasar Turkiyya, wacce ta yi barna a makwanni biyu da suka gabata. 

Har ila ya, a yankin Siriya, akalla mutane shida ne suka mutu a Aleppo daga baraguzan gini yayin da a kasar Turkiyya kuwa, gine-gine masu yawa suka ruguje tare da danne dubban mutane.

Duk da cewa babu wasu rahotanni da ke bayyana rasa a rai a sabuwar girgizar, amma wata kafar yada labarai ta Turkiyya, Anadolu ta ce, girgizar ta shafi kasashen Siriya, Jordan, Isra’ila da Masar. 

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar Yanayi ya sauya bayan samun girgiza ta biyu 

An ruwaito cewa, mutanen da lamarin ya faru a yankinsu sun rasa wutar lantarki da sabis na yanar gizo, kuma mutane da yawa ne suka fice daga gidajensu zuwa budaddun wurare don gudun rugujewa gine-gine.

 Hukumomin kasar Siriya sun ankatar da ‘yan kasar da su bi ka’idojin da gwamnati ta gindiya tun faruwar girgizar kasar farko tare da ba da hadin kai wajen ceto wadanda gine-gine suka danne.

Post a Comment

0 Comments