Advertisement

Responsive Advertisement

Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Jam’iyyun Adawa da ‘Yan Takararsu a Mintin Karshe


 A yau aka ji Jam’iyyun ZLP, NRM, APP, APM a Legas sun ce Bola Tinubu ne ‘dan takaransu a 2023 

Shugabannin jam’iyyun za su marawa Bola Tinubu/Kashim Shettima baya su karbi mulkin Najeriya 

‘Yan adawan sun lissafo hujjojin da suka jawo su ke ganin cancantar Jagaban kan sauran ‘yan takara 

Lagos - Jam’iyyun siyasa akalla goma da kuma ‘yan takararsu suka yi wa Bola Tinubu mubaya’a, su na goyon bayan ya zama shugaban kasa. 

Rahoton Tribune ya ce jam’iyyun nan sun hada da ZLP, NRM, APP, APM da sauransu, sun bayyana haka a wani taro da aka yi a Ikeja a jihar Legas. 

Shugabar jam’iyyar hamayya ta NRM ta reshen Legas, Temilola Akinade ta ce sun tsaida ‘dan takaran ne domin sun fahimci shi ya fi cancanta.

 Akinade tayi jawabi a asibitin filin tashin jirgin Ikeja a madadin sauran shugabannin jam’iyyu ta ce sun yi mubaya’a ne ga tikitin Tinubu/Shettima.

Shugabar jam’iyyar hamayya ta NRM ta reshen Legas, Temilola Akinade ta ce sun tsaida ‘dan takaran ne domin sun fahimci shi ya fi cancanta. 

Akinade tayi jawabi a asibitin filin tashin jirgin Ikeja a madadin sauran shugabannin jam’iyyu ta ce sun yi mubaya’a ne ga tikitin Tinubu/Shettima


Post a Comment

0 Comments