Advertisement

Responsive Advertisement

Yamma Sun Watsar da Obi, Sun Koma Bayan Tinubu a 2023

Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya kama hanyar mamaye kuri'un arewa maso gabas 
Mambobin jam'iyyar LP da masu neman takara a shiyyar sun ayyana cikakken goyon bayansu ga tsohon gwamnan Legas
 A ranar Asabar mai zuwa, 25 ga watan Fabrairu, 2023, hukumar INEC zata gudanar da zaben shugaban kasa.

Kwanaki kalilan gabanin babban zaɓen 2023, mambobin Labour Party a arewa maso yamma, sun bayyana goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu.
 Tsohon gwamnan jihar Anambra, Mista Peter Obi, shi ne yake neman zama shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar LP, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Da yake jawabi a taron manema labarai a madadin ɗaukacin mambobin LP na shiyyar arewa maso yamma, Bashir Ishaq, ya ce a shirye suke su yi aiki domin Tinubu ya kai ga nasara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar A jawabinsa ya ce:
 "Gamayyar yan takarar gwamna, Sanatoci, majalisar wakilai da majalisar jiha, shugabanni da mambobin kwamitin kamfe, mambobin kamfen ɗan takarar gwamna Kano da arewa maso yamma na LP duk mun cimma matsaya." 
"Baki ɗayanmu mun amince da goyon bayan takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Mun amince zamu maida shirinmu da tsarukan siyasar mu wajen haɗa kan al'umma har ya kai ga zama shugaban ƙasa na gaba." 

Post a Comment

0 Comments