Advertisement

Responsive Advertisement

Ɗan indiya da ke son zama shugaban Amurka


 Ya zuwa yanzu, biyu daga cikin ‘yayan jam’iyyar Republican wadanda suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugabancin Amurka mutane ne mazauna Amurka amma ‘yan asalin kasar Indiya.

Yayin da mutane suka san Nikki Haley sosai, wani da ba a san shi sosai ba shi ne Vivek Ramaswamy. Yar jarida mai zama a California, Savita Patel ta duba irin damar da yake da ita, da kuma ko akwai yiwuwar zai iya kawo sauyi.

Mr Ramaswamy, wanda hamshakin attajirin dan kasuwa ne, kuma mawallafin wani littafi da ake kira ‘Woke, Inc.’, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ne a lokacin da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Fox News, inda ya fitar da wani bidiyo yana bayani kan manufofinsa na siyasa.

Yana son ya kaddamar da wani tsari na nasarorirn da Amurka za ta iya cimmawa, kuma ya ce cakuduwar mutane masu aslai daban-daban ba ya da wani amfani matukar babu wani abu mai karfi da zai dunkule su wuri guda.

Matashin mai shekara 37, wanda aka haifa a Ohio, ya yi karatunsa ne a Harvard da kuma Yale, ya tara dukiyarsa ne ta hanyar sana’ar fasahar fitar da abubuwa masu amfani daga tsirrai, daga nan kuma sai ya kafa wani kamfanin kula da gine-gine.

Ya kasance mai yawan tofa albarkacin bakinsa game da abin da ya kira wani tsarin duniya na farga game da banbancin launin fata da kuma yanayi, lamarin da ya ce yana illa ga kasuwanci da kuma kasar ta Amurka.

Yana da ra’ayin ganin cewa Amurka ta rage dogaro a kan China ta bangarori da dama.

Ra’ayoyin Mr Ramaswamy sun yi daidai da na dan uwansa dan jam’iyyar Republican, Vikram Mansharamani, wanda ya yi takarar sanata daga New Hampshire a zaben tsakiyar zango na 20222, kuma a kwanan nan ya hadu da Mansharmani a wata ziyara da ya kawo masa.

Mr Mansharmani ya bayyana Ramswamy a matsayin mai himma, wanda ya iya kalamai, kuma mai zurfin tunani, kuma ya ce manufarsu ta hada kan al’umma a maimakon rarrabuwa, ta zo daya.

Ya ce “siyasar nuna wariya ta samu gindin zama a Amurka, kuma hakan lamari ne mai raba kawunan mutane a maimakon hada kawunansu. Ya kamata mu dubi abubuwan da muke da su wadanda suka sa muka zamo Daya. Ya kara da cewa Niki Haley ta je gidansu a New Hampshire cikin kwanakin nan.

Mr Ramaswamy da iyalinsa

ASALIN HOTON, RAMASWAMY CAMPAIGN

Bayanan hoto, 

Mr Ramaswamy da iyalinsa

To amma akwai wasu Amurkawan yan asalin indiya wadanda ba su yadda da akidar Mr Ramaswamy ba, kuma suna ganin manufofinsa ba su da kwari.

Shekar Narasimhan, wanda ya samar da kungiyar mutanen nahiyar Asiya da na yankin Pacific, ya ce duk da yana son ganin mutanen da suka fito daga Asia sun yi nisa a harkar siyasar Amurka, to amma ba ya da kwarin gwiwa a kan Mr Ramaswamy.

Mr Narasimhan ya ce ”dan kasuwa ne kuma ba ya da wani mummunan tarihi, to amma mene ne manufofinsa?” ”Shin ya damu da lafiyar tsofaffi? Mene ne manufofinsa a kan samar da manyan ayyuka? Ba ya da wata matsaya kwakkwara kuma har yanzu bai bayyana manufofinsa ba yadda suka dace.”

Ya bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a iya aiwatarwa ba, “yana da ra’ayin cewa Mr Ramaswamy na ganin cewar yana da abin da zai fada kuma za a fi jin sa idan ya ce zai yi takarar shugaban kasa.”

Mr Narasimhan ya kuma yi tambayar ko ya zuwa yanzu ba-indiyen ya amince da asalinsa a maimakon nuna cewa kamar wannan ba abu ne mai muhimmanci ba.

Yawancin al’umma magoya bayan jam’iyyar Republican sun ce bas u taba jin duriyar Ramaswamy ba har sai da ya bayyana aniyarsa ta takarar shugaban kasa.Dr Sampat Shivangi, wani shahararren dan jam’iyyar Republican kuma jigo cikin masu kokarin tara wa jam’iyyar kudi y ace “ban taba haduwa da shi ba. An da ice min yana da kudi kuma ya iya magana, to amma zai zama Daya ne kawai a cikin yan Takara masu yawa.

Sai dai wasu sun yi amanna da shi.

Danny Gaekwad, wanda ya ja ragamar gidauniyar tallafin kudin zabe na ‘yan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Democrats da dama, tun lokacin George Bush, ya ce inda shi (Ramaswany) bai fito ba cikin lokaci, babu wanda zai rinka tambayar ko shi wane ne..

DuK da Gaekwad na yaba wa kokarin Mr Ramaswamy, amma yana ganin cewar dole ne ya fitar da tsarinsa, irin tsarin da zai amfani indiyawa mazauna Amurka.

Ya kara da cewa lamarin ya yi wuri a yanzu, yana bayyana cewa za a iya samun kwararan yan takara biyu a Florida kawai.

Nikki Haley

ASALIN HOTON, GETTY IMAGES

Indiyawa mazauna Amurka na hasahsen cewa za a kara ne sosai tsakanin mutane uku, wato “tsakanin Donald Trump, da Mr DeSantis da kuma Ms Haley, shi y asa yake son ya dan dakata kadan a maimakon yin hadin gwiwa da wasu a wanna matakin, musamman ma ganin cewa har yanzu babu tabbasa a kan shari’ar da ake yi wa Donald Trump.

Mr Shivangi ya ce tsarin kazar-kazar na Ms Haley na burge shi, kuma zai goya mata baya idan aka kawar da Trump daga takarar.

Ya ce kasancewar ta a matsayin ba-amurkiya yar asalin Indiya shi ne ya sanya muke kusa da ita.

Sai dai duk da irin wadannan kalubale, al’umma mazaunan Amurka yan asalin Asia na murana da karuwar da aka samu ta ire-iren su da ke kara shiga cikin lamuran siyasa., musamman a zabuka uku da suka shude.

Mr Geakwod ya ce “abu ne mai kyau yake faruwa. Amurkawa yan asalin indiya na kara yunkurowa, kuma yana alfahari da shaharar daya daga cikin mutanensu.

Hatta abokan hamayyar ,mu sun yarda da hakan.

Mr Narasimhan ya ce “idan yaranmu za su rinak ganin wasu yaran masu suna kamar Ramaswamy, ko Khanna, ko Krishnamoorthi, kuma za su iya cin zabe, hakan yana da kyau sosai.

Post a Comment

0 Comments