Advertisement

Responsive Advertisement

Shugaban Masar ya yi alƙawarin bai wa Tinubu Haɗin kai domin aiki tare


Shugaban ƙasar Masar Abdel Fattah El-Sisi ya yi wa sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Tinubu alƙawarin ci gaba da ba shi goyon baya domin inganta alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.

A wata sanarwa da fadar shugaban Masar ɗin ta fitar ranar Lahadi, inda mista El-Sisi yake tsokaci kan zaɓukan ƙasar da suk gabata.

Sanarwar ta ƙara da cewa ''Shugaban ƙasar Masar, na miƙa saƙon taya murna ga al'umma da gwamnatin Najeriya bayan kammala zaɓukan shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki, wanda ya nuna irin ci gaban da 'yar uwarmu (Nijeriya) ta samu a fannin dimokraɗiyya''.

El-Sisi ya ce a shirye yake ya yi aiki da sabon shugaban domin ciyar da alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu gaba, tare da al'umominsu da kuma nahiyar Afirka baki ɗaya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa ƙasashen biyu na da kyakkyawar dangantaka tun shekarar 1961 lokacin da aka samar da dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu a lokacin mulkin tsoffin shugabannin ƙasashen biyu na wancan lokaci, marigayi Gamal Abdel-Nasser, da kuma Abubakar Tafawa Balewa.

Rufewa

Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

Post a Comment

0 Comments