Rundunar ฦดan sanda a jihar Kano ta sanar da kama mutum 14 waษanda take zargi da aikata fashi da makami da tu'ammali da ฦwayoyi da kuma aikata dabanci a makon farko na watan azumin Ramadan.
Rundunar ta ce an samu nasarar kama mutanen ne a wani samamen da rundunarta ta dawo da zaman lafiya ta kaddamar.
Ta ce ta kuma ฦwato muggan maฦamai da haramtattun ฦwayoyi da kuma kayayyaki da aka sata.
A wata sanarwa da kakakin runduar ฦดan sanda jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce kwamishinan ฦดan sandan jihar, Mamman Dauda ya ayyana yaki kan duk wani nau'i na aikin dabanci a faษin jihar.
ฦณan sandan sun ce suna iyaฦar kokarinsu wajen dakile dukkan ayyukan ษata-gari a jihar.
CP Mamman Dauda ya gargaษi duk masu aikata laifi da su guji yin hakan saboda za su iya fuskantar hukunci mai tsanani idan aka kama su.
Ya kuma bukaci al'umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yadda da shi ba, su kuma guji ษaukar doka a hannunsu.

Comments
Post a Comment