Babu Wanda Ya Baiwa Rarara Gida Ko Mota, Kuma Ni Ma Babu Wanda Ya Ba Ni Komai Akan Asarar Da Muka Yi, Inji Baban Chinedu.
Daga Abubakar Shehu Dokoki
Baban Chnedu ya kuma ฦara da cewa "maganar baiwa Rarara gida da mota kamar yadda wasu ฦafofin sadarwa suka yaษa duk ฦarya ne, kuma ni ma babu wanda ya ba ni koda kwano akan abinda ya faru da mu.
Baban Chinedu ya ci gaba da cews "Bana tunanin akwai ษan siyasar da zai iya biyan Rarara asarar kuษin da ya yi lokaci ษaya, akwai su, amma yin hakan ne abu mai wahala, domin ya yi asara sosai, ko ni ma nan na yi asara ta haura milyan arba'in. Kuma duk inda aka kama kaya a wurin ฦดan sanda a Kano babu inda babu kayana"


Comments
Post a Comment