Advertisement

Responsive Advertisement

Dokar jefar da jarirai a Namibia: Ina son wanda zai lura da jaririna yadda ya dace


 Tsintar gawar wata jaririya da aka ajiye a bayan wata makaranta a Windhoek babban birnin Namibia a watan Nuwambar da ya gabata ta nuna sauya doka kawai ba zai samar da abin da ake so ba wajen shawo kan matsalar.

A 2019, Namibia ta yi dokar da ke cewa duk matar da ta jefar da ɗanta saboda damuwar rayuwa ba za a gabatar da ita ba a gaban kotu.

An samar da wuraren da ya kamata a kai jarirai da iyayensu suka jefar da su, amma da alamar har yanzu akwai buƙatar wayar da kan mutane kan hakan.

Shekara biyu bayan nan, Linda wata da muka sauya sunanta ta yi amfani da irin waɗannan wurare wajen rainon ‘yarta.

Linda ta riƙa kuka lokacin da take magana kan 'yarta da ta haƙura da ita.

“A matsayina na uwa matakin da na ɗauka ba mai sauƙi ba ne, in ɗauki ‘yata na kai na ajiye a wani wuri. 

Amma na zaɓi yin hakan ne saboda yanayin da na tsinci kaina ciki,” in ji Linda cikin wata murya mai taushi. 

Ta ma yanke ƙaunar sake haihuwar wata yarinyar.

Linda na zaune ne da ‘ya’yanta da kuma saurayinta a wani ɗan ƙaramin wuri a yankin Swakopmund da suke zaune ba bisa ƙa’ida ba.

Sau da yawa ma ba ta iya cin abinci, kuma ta ce sauran 'ya'yanta huɗu na fahimta idan “mahaifiyarsu ba ta da abin da za ta ba su, ba za mu ci komai ba yau”.

Ta ƙara da cewa: “Amma na biyar ɗin idan babu abinci, ba zai fahimta ba. Sai na ga ya kamata na haƙura da wannan jariri ga wanda zai iya kula da shi yadda ya kamata.”

Linda na cikin ɓacin rai amma ta yi imanin wannan ne abin da ya dace ta yi wa ɗanta.

“Ina kewarsa saboda na shayar da shi na kimanin kwanaki uku, amma na san yana nan ƙalau, yana tare da mutanen kirki.”

Post a Comment

0 Comments