Hukumar Zaษe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta sanya Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranar ฦarasa zaษukan da ba su kammala ba a jihohi da dama na ฦasar.
A wani saฦo da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Litinin, INEC ta ce ta yanke wannan shawara ce bayan wata ganawa tsakanin manyan jami'anta.
Akwai zaษukan gwamnoni kamar a jihohin Kebbi da Adamawa, waษanda jami'an sanar da sakamakon zaษe suka ce ba su kammala ba a ranar 18 ga watan Maris, baya ga sauran zaษukan 'yan majalisun dokoki, da su ma suka fuskanci irin wannan cikas.
ฦaya daga cikin jihohi da aka samu zaษukan da ba su kammala ba masu yawa a ranar 25 ga watan Fabrairu, ita ce Sokoto, inda ake da 'yan majalisar wakilai 11 da sanatoci 3 waษanda duk zaษensu bai kammalu ba.
Masu sa-ido sun soki hukumar INEC saboda matsalolin da aka samu a zaษen shugaban ฦasa da na 'yan majalisun tarayya na ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, wanda Bola Ahmed Tinubu, ya yi nasarar zama sabon shugaban Najeriya.
Haka ma a ranar 18 ga watan Maris lokacin da INEC ta gudanar da zaษen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi, an gamu da wasu daga cikin matsalolin da aka samu a zaษen INEC na farko.

Comments
Post a Comment