Advertisement

Responsive Advertisement

Ma'aikaci Ya Gurfana Gaban Kotu Bisa Satar Kuɗin Kamfani


 Wani ma'aikacin wani kamfani a jihar Legas ya gurfana a gaban kotu saboda cin amanar kamfanin sa 

Ma'aikacin kamfanin dai yayi sama da faɗin da kuɗaɗen kamfanin waɗanda yawan su ya kai naira miliyan goma 

Ma'aikacin kamfanin ya shafawa idon sa toka yace sam bai aikata wannan laifin na sata da ake tuhumar sa da shi ba

Legas- An gurfanar da wani mutum mai suna Folarin Ajayi, a gaban wata kotun majistare mai zaman ta a Ogba, cikin Ikeja, bisa zargin satar naira miliyan goma daga wani kamfani,

 United Parcel Services, a yankin Gbagada na jihar Legas. Ajayi, wanda aka gurfanar da shi a gaban majistare O Obasa, yana fuskantar tuhumar laifi ɗaya na sata wanda ƴan sanda suke tuhumar sa da shi. Rahoton The Punch 

Post a Comment

0 Comments