Advertisement

Responsive Advertisement

Man City na zawarcin Rice, Bernardo Silva na cikin rashin tabbas


 


Manchester City ta shiga sahun masu zawarcin ɗan wasan Ingila da ke buga tsakiya Declan Rice, mai shekara 25, idan West Ham ta nuna matsuwar sayar da kyeftin din nata da aka kiyasta kuɗinsa kan fam miliyan 100.(TeamTalk)

Rice na cikin 'yan wasan da ake kyautata zaton Arsenal na hari a wannan kaka.(Times - subscription required)

Tsohon mai buga tsakiya a Manchester United Roy Keane ya ce Rice bai yi wa Hammers wasa ba a wannan kakar. (ITV, via Metro)

Makomar mai buga tsakiya a Portugal Bernardo Silva a Manchester City na cikin rashin tabbas, yayinda Barcelona ke ci gaba da sa ido kan ɗan wasan mai shekara 28, da kuma yunkurin mika tayinta idan za a bata shi a wannan kaka.(Sport - in Spanish)

Post a Comment

0 Comments