Advertisement

Responsive Advertisement

Nasarar Obi a Legas da Abubuwan ban Mamaki 10 da suka Girgiza Al’umma a Zabe


 An kammala babban zaben 2023 a fadin Najeriya, a karshe Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara 

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar da galabar APC a zaben da ya zo da abin mamaki 

Akwai abubuwan ban mamaki da suka faru wanda har gobe ‘Yan Najeriya suke magana a game da su 

Rahoton nan ya tattaro abubuwa da suka zama na ban al’ajabi a a zaben da aka gudanar, ga su nan kamar haka: 

1. APC ta rasa Legas 

Legit.ng Hausa ta kawo rashin nasarar Bola Tinubu a jihar Legas a matsayin mafi ban mamaki a zaben bana, ba kasafai ‘dan takara yake rasa mahaifarsa a zabe ba. 

2. Nasara a Aso 

Rock Baya ga galaba da LP tayi a jihar Legas a kan jam’iyyar APC, Peter Obi ya lashe zabe a duka rumfuna tara da ake da su a cikin fadar shugaban kasa da ke Abuja. 

3. Shugaban APC ya rasa nasarawa 

Ba ayi tunanin Abdullahi Adamu wanda yake ikirarin bai taba shan kayi ba zai sha kashi, a 2023 LP ta karbe Nasarawa, sannan APC ta rasa Sanata a mazabarsa. 

4. Ifeanyi Okowa ya ji kunya 

Punch ta na kawo shan kashin Dr Ifeanyi Okowa a cikin abubuwan ban mamaki. Ganin yana takara, ba ayi tunanin har ila yau LP za ta doke Gwamnan a Delta ba.

 5. Katsina ta fada hannun 

Atiku Atiku ya samu nasara a kan APC a jihar Katsina inda nan ne mahaifar Muhammadu Buhari. A zaben shugaban kasa da aka yi PDP da APC su na da 489,045 da 482,283. 


Post a Comment

0 Comments