Advertisement

Responsive Advertisement

Real Madrid na kwadayin Haaland, PSG na farautar Maguire


 Real Madrid na duba yiwuwar dauko ɗan wasan Manchester City kuma ɗan asalin Norway Erling Haaland mai shekara 22, a wani ɓangare na shirin dauko matasa da ke tashe kungiyarta, kamar yada take harin ɗan wasan Borussia Dortmund Jude Bellingham ɗan kasar Ingila mai shekara 19.(Independent)

Ɗwasan Manchester United kuma mai tsaron baya a Ingila Harry Maguire, mai shekara 30, ya kasance wanda Paris St-Germain ke kwaɗayi a kan fam miliyan 50.(Sun)

Mutumin da aka bai wa shugabanci Bayern Munich Uli Hoeness, ya ce zai kasance "abin bajinta idan kungiyar ta Jamus ta dauko ɗan wasan Tottenham, asalin kasar Ingila Harry Kane, mai shekara 29, kuma lokacin da kungiyar za ta kashe yuro miliyan 100 kan ɗan wasa ya tunkaro". (Sky Sport Germany - in German)

Manchester United ta sanya sunan ɗan wasan Chelsea da Ingila Mason Mount, mai shekara 24, cikin jeren 'yan wasan da take hari a wannan kaka. (Guardian)

Mauricio Pochettino ya shaidawa Tottenham cewa ya matsu ya koma domin maye gurbin Antonio Conte a masatyin koci, sai dai mutumin mai shekara 51 asalin kasar Argentine na da zaɓin samun wata kungiya a wajen Ingila. (talkSPORT)

Tottenham za ta tattauna kan cancantar Pochettino da Thomas Tuchel a matsayin wanda ya fi dacewa ya maye gurbin Conte, wanda kungiyar ke Shirin raba gari da shi. (Guardian)

Kocin Brentford Thomas Frank da na Fulham Marco Silva na cikin jeren mutane biyar da ake nazarin tantacewa domin maye gurbin Conte aTottenham. (Independent)

Manchester City ta shirya tsaf domin sayar da ɗan wasanta na baya kuma ɗan kasar Sifaniya Aymeric Laporte, mai shekara 28, a wannan kaka muddin ta iya farauto masu maye gurbinsa. (Football Insider)

Manchester United na ɗaya daga cikin kungiyoyi da ke nuna zawarci kan ɗan wasan Argentina mai shekara 29 Paulo Dybala, da take iya sayowa kan fam miliyan 11 a wannan kaka duk da cewa a bara ya koma Roma. (Goal)

Manchester United ta shiga jeren masu nuna kwaɗayinsu kan mai tsaron raga a Brentford David Raya, ɗan wasan mai shekara 27 na Shirin raba gari da kungiyarsa bayan watsi da sabon kwantiraginsa. (talkSPORT)

Post a Comment

0 Comments