Advertisement

Responsive Advertisement

Ronaldo zai kafa sabon tarihi a tawagar Portugal


 Cristiano Ronaldo zai kafa tarihin mafi yawan buga wa tawaga wasanni, idan ya yi wa Portugal karawa da Liechtenstein ranar Alhamis.

Portugal da Liechtenstein za su buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da Jamus za ta karbi bakunci, wato Euro 2024.

Ronaldo, mai shekara 38 ya yi kan-kan-kan da tarihin Bader Al Mutawa na Kuwai da ya yi karawa 196, shine kan gaba a duniya tun farko.

Ronaldo shima ya buga wa Portugal wasa na 196 a fafatawar da Portugal ta sha kashi a hannun Morooco a gasar kofin duniya a Qatar a 2022.

Ronaldo yana cikin 'yan wasan da sabon koci, Roberto Martinez ya gayyata, domin buga wasannin neman shiga Euro 2024

Ronaldo wanda ke taka leda a Saudi Arabia a Al Nassr - shine kan gaba a cin kwallaye a tawaga a duniya mai 118 kawo yanzu.

Tun farko an dauka Ronaldo zai yi ritaya daga buga wa Portugal tamaula, bayan da Morocco ta fitar da kasar a kofin duniya zagayen quarter finals.

A lokacin ne ya fita daga fili yana kuka a gasar da aka yi a Qatar a 2022, wadda Argentina ta lashe karkashin Lionel Messi.

Ronaldo ya ci kwallo tara a wasa 10 da ya yi wa Al Nassr, bayan da ya bar Manchester United a Nuwamba, sakamakon wata hira da ya yi har ma ya caccaki United.

Martinez ya ce Ronaldo, wanda ya fara yi wa Portugal tamaula a 2003 dan wasa ne mai mahimmaci mai kwarewa, ''bana kallon shekarunsa.''

Macen da ke kan gaba a yawan tamaula a duniya ita ce Kristine Lilly, wadda ta yi wa tawagar Amurka karawa 354.

Ronaldo ya ci gaba da kafa tarihi a fagen taka leda

Wannan tarihin zai kara daga darajar Ronaldo a matakin daya daga fitatcen dan wasa a duniya a karnin nan.

Ronaldo ya lashe kofin lik bakwai da wasu manyan ko 11 da Champions League biyar da Club World Cup hudu da European Championship daya.

Tsohon dan wasan Sporting Lisbon da Manchester United da Real Madrid da kuma Juventus ya lashe kyautar Ballon d'Or biyar da ta Best Fifa biyu.

A cikin watan Nuwamba ya ci kwallo na 800 a tarihinsa na taka leda, shine kan gaba a sharara kwallaye a tawaga da kungiyoyi.

Karin wasu bajintar da ya yi:

Kan gaba a yawan cin kwallaye a Champions League (140)

Kan gaba a yawan buga wasanni a Champions League (183)

Kan gaba a yawan lashe Champions League wins (5)

Na farko da ya ci kwallo a wasan karshe a Champions League uku

Na farko a buga wasan karshe European Championship (5)

Kan gaba a cin kwallaye a European Championship (14)

Kwallayen da ya ci a Euro da Gasar kofin duniya (22)

Kan gaba a yawan cin kwallaye a tawaga a duniya (118)

Na farko da ya ci kwallo uku rigis karo 10

Post a Comment

0 Comments