Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya zaษaษษen gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf nasarar da ya samu a zaษen gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga watan Maris.
Cikin wata wasiฦa da ya aike da ita, Sarkin Kano ya ce ya fahimci mutane sun karษi dimokradiyya hannu biyu-biyu, kuma abu mafi mahimmani shi ne yadda suka fito suka kaษa kuri'unsu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Gabanin haka shi ma Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya ya aike da ta shi wasiฦar taya murna ga sabon zaษaษษen gwamnan, wanda ya ce a madadinsa da iyalansa ya aika sakon.
Sarkin Rano ma Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa ya aike da na shi saฦon tare da fatan Allah ya taya sabon shugaban riฦo da shugabancin mutanen Kano.
Duka sarakunan sun miฦa godiya ga malaman addinai da shugabannin jama'a da suka riฦa wayar da kan al'umma, aka yi zaษe lafiya aka gama lafiya.

Comments
Post a Comment