Hukumar kula da aikin Haji da Umrah ta Saudiyya ta yi kira ga masu ziyarar ibada zuwa wurare masu alfarma da su martaba darajar wuraren.
Sannan kuma su bi dokoki wajen ษaurar hotunan.
Hukumar ta ce bai kamata masu ziyarar ibadar su ษige da ษaukar hotuna, a maimakon mayar da hankali kan ibadar da ta kai su ฦasa mai tsarkin.
Haka kuma hukumar ta gargaษi masu ษaukar hotunan da su guji haษawa da wasu mutanen a cikin hoton nasu, ba tare da izini ba.
Sannan ta bayyana cewar masu ziyarar ibadar su daina tsayawa don ษaukar hoto a wuraren da jama'a da dama suka taru, domin a cewarta hakan na janyo cunkuson jama'a a wuraren.
A baya-bayan nan dai mutane sun ษullo da salon ษaukar hotuna a lokacin ziyarar ibada zuwa ฦasa mai tsarkin tare da wallafawa a shafukansu na sada zumunta.
Lamarin da wasu malamai ke ganin cewa zai iya zama 'Riya', abin da kuma a cewar malaman zai iya ษata wa mutanen ibadar tasu.

Comments
Post a Comment