A ranar Asabar 25 ga watan Fabarairu, Najeriya ta gudanar da zaษen shugaban ฦasa da na 'yan majalisar tarayya.
Zaษen dai ya kasance mai zafi wanda rabon da aka irin haka tun bayan dawowar ฦasar mulkin dimokuraษiyya a 1999.
Sai dai sakamkon zaษen da ya fito daga wasu jihohi ya bayar da mamaki ganin cewa wurare ne da jam'iyya mai mulki ke samun nasara, amma a wannan aro ‘yan adawa ne suka ci jihohin.
Katsina
Katsina dai ta kasance mahaifar shugaban ฦasa Muhammadu Buhari, jam’iyyar hamayya ta PDP ce ta lashe zaษe a jihar, inda ta samu kuri’u 489,045 yayin da ita APC kuma ta samu 482,283.
Yobe
Wata jiha da sakamakonta ya bayar da mamaki kuma ita ce Yobe, inda nan ma jam’iyyar PDP ta lashe zaษen jihar da kuri’u 198,567 yayin da APC kuma ta samu kuri’u 151,459. Hakan ya faru duk da cewa APC ce ke mulki a jihar.
Lagos
Haka nan ma, a Legas, mahaifar ษan takarar shugaban ฦasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, jam’iyyar adawa ta Labour ce ta samu nasara a zaษen jihar da kuri’u 582,454, inda APCn kuma ta samu kuri’u 572,606. Hakan kuma ya faru duk da cewa APC ce ke mulki a jihar na tsawon shekaru.
Benue
A Benue da ta kasance jihar da PDP ke mulki, APC ce ta samu nasara da kuri’u 310,468, inda ta doke PDP wadda ta samu kuri’u 130,081. Sakamakon ya bayar da mamaki sosai ganin irin yawan sukar gwamnatin tarayya da gwamnan jihar Samuel Ortom ya sha yi.
Filato
Wani sakamakon zaษen shugaban ฦasa da bayar da mamaki shi ne na jihar Filato. Duk da cewa APC ke mulki a jihar, amma hakan bai hana jam’iyyar Labour samun nasara ba da kuri’u 466,272 yayin da APC ta zo na biyu da kuri’u 307,195.
Nasarawa
A Nasarawa ma sakamakon ya bayar da mamaki saboda duk da cewa APC ce ke mulki a jihar da kuma ta kasance mahaifar shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu, hakan bai hana jam’iyyar faษuwa ba. Jam’iyyar Labour ce ta samu nasara da kuri’u 191, 361 yayin da PDP ta zo na biyu da kuri’u 172,922, sai APC mai 147,093.
Ribas
A can Ribas ma, sakamakon ya zo mutane da dama bazata, inda jam’iyyar APC ta doke PDP da ke mulki a jihar a zaษen shugaban ฦasa, inda ta samu kuri’u 231,593 yayin da Labour ta zo ta biyu da kuri’u 175,555.
Sakamakon zaษen waษannan jihohi dai ya bayar da mamaki ainun saboda ganin cewa ba a taษa zaton za a ga irin sakamakon da aka gani ba.
Comments
Post a Comment