'Yar takarar gwamna a Adamawa ฦarฦashin jam'iyyar APC, Aisha ฦahiru Binani ta shigar da ฦara gaban kotu tana neman umarnin wucin gadi game da dambarwa zaษen jihar.
Tana dai neman Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ne ta yi fassarar doka game da matakin da hukumar zaษe ta ษauka ranar 16 ga watan Afrilu, bayan an ayyana cewa ita ce ta yi nasarar zama gwamna, a zaษen 18 ga watan Maris da kuma na cike-giษi a ranar 15 ga watan Afrilu.
'Yar takarar tana kuma neman kotu ta ba da umarni sannan ta hana INEC da jami'anta ษaukar ฦarin wasu matakai na bayyana wanda ya yi nasara a zaษukan da aka yi, har sai kotun ta yanke hukunci a kan buฦatar yin tsokacin shari'ar.
Mallam Ahmed Sajo, jami'i a kwamitin yaฦin neman zaษe Sanata Aisha Binani ya shaida wa BBC cewa sun je kotu ne don a yi musu fassarar sashe na 149 na dokar zaษe ta 2022.


Comments
Post a Comment