Wani rikicin naษin sarauta da ya ษarke a jihar Bauchi ya janyo asarar rai da dukiya mai tarin yawa
A rikicin da ya ษarke wani dattijo ya kwanta dama yayin da mutane da dama suka samu rau
Rundunarnika ฦดan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda tuni har ta ษauki matakan da suka dace
Jihar Bauchi - Rikicin sarauta a jihar ya janyo asarar ran wani dattijo tare da raunata wasu mutane da dama a cikin ฦaramar Bogoro da ke a jihar Bauchi.
Jaridar Aminiya tace ฦดan sanda sun bayyana cewa an kuma kona gidaje da dama waษanda yawan su aฦalla zai kai aฦalla 64, a rikicin wanda ya ษarke a daren Asabar, 15 ga watan Afirilun 2023.

Comments
Post a Comment