Hukumar zaษe a Najeriya ta sanar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaษen jihar Adamawa, wanda ya ฦare cikin taฦaddama.
Jami'in sanar da sakamakon zaษen gwamna na Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaษen ne da ฦuri'a, 430, 861.
Gwamnan mai ci ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa Aisha ฦahiru Binani wadda ta samu ฦuri'a, 398, 788.
Wannan nasara ta bai wa Fintiri ikon ci gaba da mulkin jihar Adamawa a wa'adi na biyu.
Da yammacin Talata ne, jami'in sanar da sakamako, Farfesa Mohammed Mele cikin rakiyar wasu manyan jami'an INEC na ฦasa, ya isa zauren karษar sakamako da ke Yola, inda ya ci gaba da aikin tattara sakamakon ฦananan hukumomin da suka rage.
A ranar 15 ga watan Afrilu ne, hukumar zaษe ta gudanar da cikon zaษen cikin wasu rumfuna da ke faษin ฦananan hukumomin jihar 20.
An sake kaษa ฦuri'u ne a tashoshin zaษe 69.
Sakamakon zaษen da aka ฦarasa ya nuna cewa 'yar takarar jam'iyyar APC, Aisha Binani ta samu ฦuri'a 6,513, yayin da Gwamna Fintiri na PDP ya samu 9,337.
Zaษen dai ya gamu da taฦaddama bayan kwamishinan zaษe na jihar Adamawa Hudu Ari ya sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaษen ba tare da ya fayyace sakamakon kowacce jam'iyya dalla-dalla ba.


Comments
Post a Comment