Advertisement

Responsive Advertisement

RA'AYI: Shawara Ga Iyayen Young Sheikh Zaria, Game Da Wa'azin Da Yake Yi




 RA'AYI: Shawara Ga Iyayen Young Sheikh Zaria, Game Da Wa'azin Da Yake Yi 


Daga Comr Abba Sani Pantami 


Ilmi da yarinta ba laifi bane, amma wa'azi sai an girma domin ko da ilmi sai da nutsuwa, duk wani al'amari indai Yara ne za su yi shi to tabbas sai kaga kwan-gaba kwan-baya a cikin shi sai an samu matsala.  


Musulunci bai hana Yara yin karatu ba, amma su karantar gaggawan me suke yi? Ko Annabawa da suka fi kowa hankali da tunani sai sun cika shekaru 40 sannan Ubangiji yake umurtarsu da su fara wa'azi.  


Shiyasa za kuga akwai yarinta a cikin zancenshi sosai, Yaro karami sai ka ga ya zagi wancan ya soki wancan a wurin wa'azi, ya kamata ku sani kujerar wa'azi ko da girma da hankali ya ake karewa da ka fara wa'azi anja maka Aya guda zuwa biyu an fara maka Kabbara sai ka hau tsuma in baka yi sa'a ba sai ka saki Titi ka shiga Daji ka yita Katobara a wurin wa'azin.  


Kadan daga cikin jawabi na jan hankalin da Sheikh Abubakar Lawan Triumph yayi ga iyayen Young Sheikh Zaria akan wa'azin da Yaron yake yi.  


Hakika wannan shawarine mai kyau da aka bawa iyayen Young Sheikh, idan har za'a yi duba da Maslaha ta addini, wannan shawarin babu batun yiwa yaron hassada ko bakin ciki a cikin shi.   


Allah yasa iyayen Young Sheikh su dauki wannan shawarin kuma suyi aiki dashi don gujewa wasu kura-kurai da ka iya faruwa a nan gaba.

Post a Comment

0 Comments