Ma'aikatar cikin gida a Faransa ta ce kimanin ฦดan sanda 108 ne suka jikkata sanadin arangamar da ta kaure a sassan ฦasar inda masu zanga-zanga ke nuna fushinsu kan sauye-sauyen da aka yi wa tsarin pensho.
Gerald Darmanin ya ce ba kasafai aka cika samun irin haka ba - ฦดan sanda da dama su ji rauni. Ya ฦara da cewa an kama mutum 291 yayin tashin hankalin.
Dubban jama'ar ฦasar ne suka shiga gangamin ranar Ma'aikata domin nuna adawarsu da sauye sauyen da Shugaba Emmanuel Macron ya yi.
Akasarin gangamin an yi shi lami lafiya amma an samu wasu masu tsatsauran ra'ayi da suka riฦa wasan wuta. ฦณan sanda kuma sun mayar da martani ta hanyar wulla hayaฦi mai sa hawaye da yi musu feshin ruwa.
Zuwa yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka ji rauni ba.
Wannan ne gangami na baya-bayan nan da aka yi kan ษaga shekarun fara karษar pensho daga 62 zuwa 64. ฦungiyoyin ฦwadago na son a janye matakin.

Comments
Post a Comment